Isa ga babban shafi
Iraqi

Iran ta yi wa Mayakan IS ruwan wuta a Iraqi

Kasar Amurka ta sanar da cewar jiragen saman yakin kasar Iran sun kai hare haren sama kan mayakan IS da ke da’awar Jihadi cikin kasar Iraqi, a wani yanayi da ake gani na hadin kai tsakanin kasashen biyu.

jirgin yaki mai suna F4-Phantom da ke luguden wuta a Syria
jirgin yaki mai suna F4-Phantom da ke luguden wuta a Syria REUTERS/ Osman Orsal/Files
Talla

Harin ya tabbatar da jingine banbancin ra’ayi da ke tsakanin Iran da Amurka domin hada karfi don murkushe masu tayar da kayar bayan da ke yi wa yankin barazana.

Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka John Kirby ya ce duk da ya ke ba tare suke aikin da Iran ba, sun yaba da matakin.

Akwai taron kasashen da ke adawa da ayyukan IS wanda Amurka zata jagoranta a hedikwatar kungiyar NATO da ke birnin Brussels.

Wata majiya tace taron zai tattaunawa matakan Soji da kasashen zasu dauka domin yakar mayakan IS da suka mamaye wasu yankuna a Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.