Isa ga babban shafi
Faransa-Falasdinu

Majalisar Faransa ta amince da ‘yancin Falasdinawa

Majalisar Kasar Faransa ta amince da ‘Yancin Falasdinu a matsayin kasa bayan kuri’ar da aka kada inda ‘Yan Majalisu 339 suka goyi baya, 151 suka kada kuri’ar kin amincewa. Tuni Isra’ila ta yi watsi da matakin tana mai cewa zai kara lalata yunkurin komawa teburin tattaunawar sasanta rikicin gabas ta tsakiya.

'Yan Majalisar Faransa suna kada kuri'ar amince da 'yancin Falasdinawa
'Yan Majalisar Faransa suna kada kuri'ar amince da 'yancin Falasdinawa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Faransa yanzu ta bi sahun Spain da Birtaniya da Sweden da suka amince a ba Falasdinawa ‘yanci, inda kasashe ke ganin ita ce hanyar samar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila.

Dangantakar Faransa da Falasdinawa

A shekarar 1974 ministan harkokin wajen Faransa na wancan lokaci Jean Sauvagnagues ya zama babban jami’I daga wata kasar Yammacin duniya da ya gana da shugaban Falasdinu Yasser Arafat a Beirut.

A shekarar 1975, Faransa ta zama kasa ta farko da ta bai wa kungiyar Falasdinu damar bude ofishin yada labarai a Paris, daga bisani a shekarar 1989 aka daga darajarsa zuwa ofishin tawagar Falasdinu a shekarar 1989 da kuma ofishin hulda a shekarar 2010.

A shekarar 1982 shugaba Francois Mitterand lokacin da ya ke jawabi ga majalisar Isra’ila ya bayyana muhimmancin bai wa Falasdinu kasa ta kansu.

Har ila yau a cikin shekarar 1982 Faransa ta yi amfani da karfinta wajen kwashe shugaba Arafat da sojojinsa a Beirut lokacin da sojojin Isra’ila suka musu kawanya.

A shekarar 1989 shugaba Mitterand ya karbi Yaseer Arafat a ziyarsa ta farko zuwa Paris.

A shekarar 2004 shugaba Jacques Chirac ya bai wa Arafat damar zuwa Faransa don jinya bayan Isra’ila ta killace shi a Ramallah inda ya yi ta fama da rashin lafiya, jinyar da ta yi sanadiyar rasuwarsa.

A shekarar 2012 shugaba Francois Hollande ya bukaci kafa kasar Falasdinu kusa da ta Isra’ila da kuma dai na gine gine a Yankunan Falasdinawa.

A shekarar 2014 Faransa ta bukaci kasashen duniya da su magance rikicin isra’ila da Falasdinu cikin shekaru 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.