Faransa zata amince da ‘Yancin Falasdinawa
‘Yan Majalisun kasar Faransa daga bangaren Jam’iyar gurguzu na shirin gabatar da wani kudiri da zai bukaci gwamnatin kasar ta amince da kasar Falasdinu makwanni bayan Majalisar kasar Birtaniya ta amince da haka. Bukatar ta biyo bayan rushewar tattaunawar zaman lafiyar da ake tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da kuma yakin da aka yi a Gaza wanda ya kai ga kashe Falasdinawa sama da 2,000.
Wallafawa ranar:
Majalisar Faransa ta bukaci gwamnatin kasar ta yi amfani da makamin amincewa da kasar Falasdinun wajen tilastawa Isra’ila kawo karshen gine ginen da ta ke yi a Yankunan Falasdinawa.
Kasar Sweden ce kasa ta farko a Turai da ta sanar da amincewa da kasar ta Falasdinu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu