Isa ga babban shafi
Ukraine-Algeria

Jirgin Ukraine ya yi hatsari a Algeria

Wani jirgin saman kasar Ukraine mai dakon kaya ya yi hatsari a yankin Sahara da daren Assabar, kuma mutane bakwai da ke cikin jirgin dukkaninsu sun mutu, kamar yadda mahukuntan kasar Algeria suka tabbatar. Ma’aikatar sufuri a Algeria tace Jirgiin ya yi hatsari ne a kusa da filin saukar jirage na Tamanrasset da misalin karfe 2:40 na dare akan hanyarsa daga birnin Glasgow na kasar Scotland zuwa kasar Equatorial Guinea.

Taswirar yankin Tamanrasset a kasar Algeria
Taswirar yankin Tamanrasset a kasar Algeria RFI
Talla

A cikin Sanarwar da hukumar Sufurin ta fitar tace babu wanda ya rayu a cikin jirgin bayan Jami’an agaji sun isa inda ya fadi.

An bayyana cewa jirgin yana dauke ne da kayan hako man fetir, kuma ya nemi ya yada zango ne a Algeria saboda tangardar na’ura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.