Isa ga babban shafi
Ukraine-Malaysia

MH17: An Zargi ‘Yan tawayen Ukraine da boye gaskiya

Gwamnatin kasar Ukraine ta zargi ‘Yan tawayen kasar da ke kishin Rasha da boye wasu hujjoji da zasu tabbatar da harbo jirgin Malayasia MH17 aka yi da makami mai linzami a yankin da ‘Yan tawayen suke iko.

Talla

Tawagar masu sa ido ta Turai su kimanin 30 sun ce ‘Yan tawayen sun ba su damar sa Ido ne kawai ga filin da Jirgin ya tarwatse tare da takaita masu gudanar da kwakkwaran bincike a yankin da jirgin ya tarwatse.

Cikin wata sanarwa, gwamnatin kasar Ukraine tace ‘Yan tawayen masu samun goyon bayan kasar Rasha suna kokarin boye gaskiya tare da tarwatsa dukkanin wasu hujjoji da zasu kama su da laifin aikata wannan mummunan al’amari da ya sabawa dokokin duniya.

Ukraine tace ‘Yan tawayen sun boye wani bakin akwati na nadar bayanai a cikin jirgin tare da kwashe gawawwakin wasu mutanen da ke cikin jirgin kimanin 38 zuwa yankin Donetsk.

Sai dai shugaban ‘Yan tawayen Oleksandr Borodai ya karyata zargin.

A ranar alhamis ne dai Jirgin Malaysia mai suna MH17 ya fadi ne a yankin gabacin Ukraine kusa da kan iyaka da Rasha, bayan ya taso daga birnin Amsterdam na Netherlands zuwa Kuala Lumpur na Malaysia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.