Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Jirgin Malaysia ya yi hatsari a kasar Ukraine dauke da mutane 300

Wani jrgin saman fasinjan kasar Malaysia ya yi hatsari a sararin samaniyar kasar Ukraine, inda ya kashe illahirin fasinjoji da kuma ma’aikatansa da a jimilce yawansu ya haura 300.

Tarkacen jirgin Boeing 777 na kasar Malaysia da ya yi hatsari a ranar 17 Yuli 2014 cikin kasar Ukraine.
Tarkacen jirgin Boeing 777 na kasar Malaysia da ya yi hatsari a ranar 17 Yuli 2014 cikin kasar Ukraine. REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Lamarin dai ya faru ne a wani yanki da ke karkashin kulawar ‘yan tawayen kasar ta Ukraine, yayin da wasu ke zargin cewa ‘yan tawayen ne suka harbo shi.

Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya shaida wa shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko cewa Amurka a shirye za ta taimaka wa domin tabbatar da musabbabin faruwar wannan hatsari da rutsa da wannan jirgi da ya taso daga birnin Amsterdam na kasar Holland a kan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Haka zalika jagoran ‘yan tawayen kasar ta Ukraine mai suna Alexander Borodai, ya ce su ma za su tsagaita wuta domin bai wa jami’ai damar isa ga inda jirgin ya fadu domin yin bincike.

Tuni dai hukumar zirga zirgar jiragen sama ta kasashen Turai ta sanar da rufe hanyar da ke ratsa sararin samar kasar ta Ukraine sakamakon faruwar wannan lamari, yayin da manyan kamfanonin jiragen sama a kasashen duniya daban daban suka sanar da karkata akalar jiragensu daga yankin saboda fargabatar da ta biyo bayan faruwar wannan hatsari.

Kamfanonin jiragen sama na Air France na Faransa, Delta Air Lines na Amurka da kuma Lufthansa na kasar Jamus na daga cikin wadanda suka dauki irin wannan mataki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.