Isa ga babban shafi
Malaysia-Ukraine

Amurka tace harbo Jirgin Malaysia aka yi a Ukraine

Kasashen duniya da dama sun bayyana alhininsu game da hadarin jirgin Malaysia a yankin Ukraine inda daukacin mutanen da ke cikin jirgin 298 suka mutu. Amurka tace harbo jirgin aka yi a gabacin Ukraine tare da neman a gudanar da kwakwaran bincike.

Mutane suna zuba faranni a harabar ofishin jekadancin Holland ga wadanda suka mutu a hadarin jirgin Malaysia MH17 da ya rikito a yankin Ukraine.
Mutane suna zuba faranni a harabar ofishin jekadancin Holland ga wadanda suka mutu a hadarin jirgin Malaysia MH17 da ya rikito a yankin Ukraine. REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Gwamnatin Ukraine ta zargi ‘Yan tawayen da suka mamaye gabacin kasar, yayin da kuma ‘Yan tawayen ke zargin dakarun Ukraine.

A jiya Alhamis ne wani jirgin saman fasinjan kasar Malaysia mai suna MH17 ya yi hadari a sararin samaniyar kasar Ukraine, inda ya kashe ilahirin fasinjoji da kuma ma’aikatansa da a jimilce yawansu ya haura 298.

Jirgin ya taso ne daga birnin Amsterdam na kasar Netherlands akan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Lamarin kuma ya faru ne a Grabove, wani yanki da ke karkashin kulawar ‘yan tawayen kasar Ukraine, yayin da wasu ke zargin cewa ‘yan tawayen ne suka harbo jirgin.

Bayanai da na nuni da cewa mutane 100 daga cikin fasinjonin, kwararru ne kan sha’anin kiwon lafiya da masu fafutuka, wadanda ke kan hanyarsu ta halartar wani taro kan yaki da cutar kanjamau da ya kamata a fara karshen wannan mako a birnin Melbourne na kasar Australia.

Hukumomi a kasar Netherlands inda jirgin ya taso, sun bayyana cewa mutane 154 daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wannan hadarin ‘yan kasar ne.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ke zantawa ta wayar tarho da Firaministan kasar Netharlands jim kadan bayan faruwar wannan lamari, ya bayyana cewa Amurka a shirye ta ke domin kaddamar da bincike da nufin gano musababbin faruwar wannan lamari da ya yi matukar girgiza kasashen duniya.

Cikin Fasinjan jirgin akwai ‘Yan Malaysia da Australia da Indonesia da Birtaniya da Jamus da Belgium da Phillippins da kuma kasar Canada.

Jagoran ‘yan tawayen Ukraine Alexander Borodai, ya ce a shirye suke su tsagaita wuta domin isa ga inda jirgin ya fado domin gudanar da bincike.

Tuni dai hukumar zirga zirgar jiragen sama ta kasashen Turai ta sanar da rufe hanyar da ke ratsa sararin samar kasar ta Ukraine sakamakon faruwar wannan lamari, yayin da manyan kamfanonin jiragen sama a kasashen duniya daban daban suka sanar da karkata akalar jiragensu daga yankin saboda fargabar da ta biyo bayan faruwar wannan hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.