Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Ana jimamin mutuwar daliban Koriya ta Kudu

Dubban mutane ne suka yi ta zubar da hawaye a lokacin da aka yi zaman jimamin mutuwar daruruwan dalibai da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwan kasar Koriya ta Kudu. 

Iyalai da 'yan uwan wadanda suka mutu a hadarin jirgin Koriya ta Kudu
Iyalai da 'yan uwan wadanda suka mutu a hadarin jirgin Koriya ta Kudu DR 中文网络照片
Talla

Zaman jimamin ya auku ne a daidai lokacin da aka shiga mako na uku ana binciken sauran daliban da hadarin ya rutsa da su.

Yanzu haka adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu ya kai 150 yayin da ake ci gaba da neman mutane 152, inda ake kyautata tsammanin suna makale a cikin jirgin da ya nutse.

Akalla dalibai kusan 280 daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su dalibai, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa hutu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.