Isa ga babban shafi
Koriya ta Kudu

Shugabar Koriya ta Kudu ta soki matuka jirgin da ya kife a Teku

Shugabar Kasar Koriya ta Kudu, Park Geun-Hye ta bayyana alhininta akan dimbin hasarar rayukan da aka samu sanadiyar kifewar jirgin ruwa a teku tare da yin kakkausar suka ga tawagar matuka jirgin da suka fice a lokacin da jirgin ke nutsewa a ruwa.

Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye tana ganawa da 'Yan uwan fasinjan da jirginsu ya nutse a teku.
Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye tana ganawa da 'Yan uwan fasinjan da jirginsu ya nutse a teku. REUTERS/Yonhap
Talla

Shugabar tace wannan matsayi ne na kisa da ba zasu amince da shi ba. Geun-Hye tace zuciyarta da na al'ummar kasar sun buga kan abinda ya faru, musamman rawar da matukin jirgin ya taka na jinkirta kwashe fasinjojin jirgin lokacin da ya fara nitsewa.

Iyalan fasinjojin jirgin sun soki matakan agajin gaggawa da aka dauka wajen ceto mutane 476 da ke cikin jirgin, inda suka yi zargin gazawa daga bangaren hukumomin kasar.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da tsamo gawawaki daga cikin jirgin. Tuni kuma aka kama matukin jirgin ruwan Lee Joon-Seok tare da abokan aikinsa.

Jirgin ruwan ya nutse ne a teku kwanaki biyar da suka gabata dauke da fasinja 476, galibinsu dalibai 'Yan makaranta da malamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.