Isa ga babban shafi
Ukraine-Geneva

An cim ma yarjejeniyar sasanta rikicin Ukraine

Kasar Rasha da Ukraine da wakilan kasashen Yammaci sun cim ma yarjejeniyar sasanta rikicin kasar Ukraine, amma Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana shakku akan Rasha tare da yin barazanar karfafa takunkumi idan har aka samu cikas daga bangarenta.

Sergeï Lavrov Ministan harakokin wajen Rasha
Sergeï Lavrov Ministan harakokin wajen Rasha REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Bangarorin sun amince ‘Yan a ware a gabacin Ukraine da ke son komawa ikon Rasha su fice daga gine gine gwamnati da suka karbe iko tare da mika makamansu domin kare rayukan al’umma.

Bayan cim ma yarjejeniyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana fatar bangarorin zasu cim ma bukatun da aka shata a yarjejeniyar.

Amma Shugaba Obama na Amurka yace ba zasu yi dogaro da yarjejeniyar ba sai idan sun ga alamu a nan gaba.

Tun bayan da kasar Rasha ta mamaye yankin Crimea a watan da ya gabata, Amurka da sauran kasashen yammci suka sa kafar wando guda da ita inda suka kakaba wa Manyan Jami’anta takunkumi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.