Isa ga babban shafi
Iraqi

Hari ya kashe Jami’an tsaro 11 a Iraqi

Wani harin bam ya yi sanadiyar mutuwar Jami'an tsaro 11 a kasar Iraqi. Wadanda suka mutu din sun hada da Soji 6 da ‘Yan Sanda 5.Harin dai yazo ne kwana daya bayan da aka kashe wasu mutum 33, mafi yawancinsu jami’an tsaro.  

Wani waje da aka kai hari a kasar Iraqi
Wani waje da aka kai hari a kasar Iraqi REUTERS/Stringer
Talla

Akalla dai mutum 50 ne aka kashe 37 daga cikinsu jami’an tsaro a tashin hankali na farko da aka gudanar cikin kwanaki uku.

Wani bam da aka dana a bakin hanya ya a ranar Lahadi ya kashe sojoji hudu, cikinsu harda Manjo, ya kuma raunata wasu biyu.

Haka kuma wasu dauke da bindiha sun bude wuta akan wani shingen ‘Yan Sandaa Baquba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘Yan Sanda hudu, kamar yadda wani Asibiti ya bayyanawa Kamfanin Dillamcin labarn AFP.

Hukumomi sun bayyana cewa a watan Yuli kadai, mutane 325 su ka rasa rayukansu wanda hakan ya sa ya zama watan da mutane su ka fi mutuwa tun watan Agustan shekarar 2010.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.