Hukumar ‘Yan Sanda ta Duniya ta bukaci Cafke Mataimakin Fira Ministan Iraqi
Hukumar ‘Yan Sanda ta Duniya ta fitar da sanarwar bada umurnin Cafke Mataimakin Fira ministan Iraqi Tareq al-Hashemi wanda bisa zargin shi da taimakawa da bada tallafin kudi ga ayyukan ta’adanci.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta nemi goyon Mambobinta kasashe 190 domin taimakawa wajen inda yake buya domin Cafke shi.
Mista Hashemi dai ya taba gurfana a gaban Kotun Iraqi a Bagadaza, tare da wasu dogaran shi da ake zargin sun kashe Alkalai Shida da wasu Jami’an gwamnati.
Ana dai hasashen yanzu haka Hashemi yana cikin kasar Turkiya.
Zarge-zargen da ake wa Hashemi sun yi kokarin haifar da rikicin Siyasa a Iraqi inda magoya bayansa ‘Yan Sunni suka kauracewa majalisa akan zargin Fira Minista Nuri al-Maliki Mabiyi Shi’a da kokarin yin ruwa da tsaki wajen tafiyar da gwamnatin kasar bayan bada sammanin kamo Hashemi a watan Disemba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu