Isa ga babban shafi
Iraqi

An samu hasarar rayuka sanadiyar Jerin bama-bamai a Iraqi

Wasu jerin hare haren kunar bakin wake da aka kai a wajen bukin Mibiya Shi’a sun yi sanadiyar hasarar rayuka sama da 40 tare da raunata mutane da dama a sassan yankunan kasar Iraqi, kamar yadda Jami’an kiyon Lafiya suka tabbatar.

Wasu mazauna birnin Bagadaza sun taru a wajen da wani dan kunar bakin ya dala bom inda mabiya shi'a ke gudanar da buki
Wasu mazauna birnin Bagadaza sun taru a wajen da wani dan kunar bakin ya dala bom inda mabiya shi'a ke gudanar da buki REUTERS/Saad Shalash
Talla

Mabiya Shi'a dai suna gudanar da Bukin tuna mutuwar imam Moussa al-Kadhim ne jinin Manzon Allah (SAW) wanda bukin ya sabawa mabiya Sunni.

Rahotanni sun ce, harin kunar bakin waken farko ya auku ne a wani wurin cin abinci a Hilla, inda mutane shida suka mutu, sama da mutane 20 suka samu raunuka.

Jami’an tsaro sun ce an samu mutuwar Mutane 12 a wasu hare hare bama bamai guda Tara da aka kai a birnin Bagadaza wadanda kuma suka raunata mutane da dama.

Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda yace an samu kunar bakin wake a birnin Baquba a yankun Divala wanda ya kashe mutane Biyar tare da rauanta wasu mutane 15.

A yankin Al Azizyah, wani Kaftin na ‘Yan sanda yace an samu mutuwar mutane Biyu wasu kuma da dama suka samu rauni sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai da Mota.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.