Isa ga babban shafi
Chadi-Najeriya

Chadi na son hadin kan Najeriya don yakar Boko Haram

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya nemi a kara samar da hadin kai tsakanin dakarun hadin guiwar da ke yaki da Mayakan Boko Haram da ke barazana ga yankin kasashen tafkin Chadi. Shugaban yace duk da cewa an illata kungiyar Boko Haram, amma har yanzu ba za a iya cewa an kawo karshenta ba.

Shugaban Chadi Idriss Déby tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan à Ndjaména
Shugaban Chadi Idriss Déby tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan à Ndjaména AFP PHOTO / BRAHIM ADJI
Talla

Deby wanda ya kawo ziyara Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya ya ce in har ana so a kama shugaban kungiyar Abubakar Shekau, ya zama wajibi sojojin kasashen yankin tabkin Chadi su yi aiki tare.

Kasashen Chadi da Kamaru da Nijar sun shiga yaki da Boko Haram ne domin murkushe ayyukan kungiyar da ke barazana ga kasashensu.

Sojojin Chadi tare da Nijar da Kamaru sun taimakawa Najeriya kwato yankunan da Mayakan Boko Haram suka kwace tare da ceto ‘yan mata da yara da dama da mayakan ke garkuwa da su a Dajin Sambisa.

Shugaban Chadi dai ya dade yana sukar gwamnatin Goodluck Jonathan da wa’adin mulkinsa ke dab da kawo karshe.

“Na yi amannar cewa da mun hada kai da tuni mun kama Shekau tare da kakkabe mayakansa” in ji Shugaban Chadi Idris Deby.

Majalisar Dinkin Duniya tace adadin mutane 15,000 suka mutu sakamakon rikicin Boko Haram sannan adadin mutane Miliyan guda da rabi suka kauracewa gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.