Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kai hari a wasu yankuna Nijar

Mutane biyar ne ‘yan kungiyar boko haram suka kasha a kauyen kukwadu da ke yankin Boso a jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar, tare da kona gidaje da dama, bayan wani hari da suka kai a kauyen dake kilomita 30 a yammacin garin Boso.

Sojojin Nijar masu fada da Mayakan Boko Haram.
Sojojin Nijar masu fada da Mayakan Boko Haram. AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Rahotannin dai sun ce, Mayakan na Boko Haram sun kai harin ne a daren talata wayewar Laraba da misali Karfe 8 na dare a kauyen na koukwodou, inda sukayi amfani da harin wajen kwasar abinci a gidajen mutane sannan da cikin sauran ‘yan shagunan da suka rage a kauyen

Duk da cewa kawo yanzu, hukumomin Nijar basu bayyana adaddin mutanen da suka rasa rayukansu ba
Lamido Mumuni Haruna dan majalisar dokokin yankin Diffa yace mutane biyar ne suka mutu, wasu 2 kuma suka jikata sannan ‘yan Boko Haram din sunyi awon gaba da motoci 9 da kuma kona gidaje da dama

Kauyen kilbouwa, ma dake kusan garin da kukwadu ya fuskanci harin na ‘yan Boko Haram inda can ma suka kona gidaje da dama

Rahotanin dai na cewa, wadanda ‘yan Boko Haram din suka kashe dukaninsu fararran hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.