Isa ga babban shafi
Najeriya

An ceto Mata 293 a Dajin Sambisa

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto ‘Yan mata kimanin 200 tare wasu manyan Mata guda 93 a dajin Sambisa sansanin mayakan Boko Haram a Jihar Borno, sai dai kuma sanarwar ta ce babu ‘yan matan Chibok daga cikin wadanda aka ceto.

Wasu 'Yan Matan Chibok da suka tsere daga hannun Boko Haram
Wasu 'Yan Matan Chibok da suka tsere daga hannun Boko Haram AFP PHOTO/STR
Talla

Sojojin sun ceto matan ne a jiya Talata, kamar yadda kakakin rundunar Sojin Kanal Usman ya tabbatarwa RFI Hausa.

Kanal Usman yace dakarun kasar na musamman na kan ci gaba da kai farmaki a Sambisa inda ake hasashen nan ne sansani na karshe da Mayakan Boko Haram ke gudanar da ayyukansu.

Kuma ya ce dakarun sun tarwatsa sansanin ‘Yan Boko Haram guda hudu da suka hada da Tokombere a Sambisa.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne Mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da ‘yan matan makarantar garin Chibok 276 a Jihar Borno. Amma 57 daga cikinsu sun tsere daga hannun Mayakan.

01:41

Kanal Sani Usman Kukasheka

Bashir Ibrahim Idris

Kanal Usman ya ce ba ‘Yan Matan Chibok ba ne dakarun Najeriya suka kubutar, wasu ne daban da mayakan Boko Haram ke garkuwa da su.

A cikin wani hoton Bidiyo, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito yana ikirarin cewa ya aurar da wasu daga cikin ‘yan matan Chibok tare da sayar da saura a kasuwar bayi

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty Internetional tace kimanin mata 2000 ne mayakan Boko Haram suka sace tun bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.