Isa ga babban shafi
Najeriya

Masana sun ce ya kamata a tuhumi TB Joshua gaban kotu

Wasu masana 5 ‘yan Najeriya da ke zaune a Amurka sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta tuhumi Pastor TB Joshua da ginin cocinsa ya rufta har ma ya kashe mutane 115 a birnin Lagos.

Fasto TB Joshua
Fasto TB Joshua
Talla

Masanan sun ce ginin ya rufta ne saboda rashin ingancinsa da kuma kin bin ka’idojin gini a kasar kuma hakan na a matsayin saba wa doka.

Daya daga cikin masanan Ebanezer Obadaere ya shaida wa Radio Faransa RFI cewa, TB Joshua ya kara ginin mujami’ar ne ba tare da izinin hukuma ba, sannan kuma suna da shaidar da ke tabbatar da cewa faston ya hana ma’aikatan agaji kai dauki ga wadanda lamarin ya rutsa da su a kan lokaci.

Shi dai Pastor TB Joshua ya ce wani jirgi ne ya bi ta kan ginin kafin ya fadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.