Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Afrika ta Kudu zata gudanar da bicinke kan TB Joshua

Kasar Afruka ta kudu ta aiko da tawagar kwararru da suka hada da Likitoci, da jami’an jinya, da na Soji akan wani Jirgi Samfurin C-130 domin yin bincike kan yawan ‘yan kasar da suka mutu a cikin hatsari Coci,Afrika ta kudu ta sanar da kwashe wadanda suka jikkata zuwa gida, inda suka bayyana cewar akalla mutane 115 ne suka mutu .

Tarkacen Cocin da ta rushe a Lagas dake Najeriya
Tarkacen Cocin da ta rushe a Lagas dake Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Wani Minista a kasar Jeff Radebe da ya jagoranci tawagar kwararrun da suka gudanar da binciken ya bayyana cewar daga cikin mutanen akwai ‘yan kasar sa 84.
Kwanaki 10 da ruftawar Cocin, Afruka ta kudu ta lura, da abinda ta kira wata rufa-rufa da ta ce jami’an cocin suke ta hanyar hada Baki da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya domin hana fitar bayannai na yawan wadan da suka mutu.
Jami’an Afruka ta kudun dai sun ce akalla ‘yan kasar 350 ne ke ziyartar Cocin da aka yi gangancin budawa ba tare da an kammalata ba.

A kwanan nan dai an bayyana yunkurin da mai Cocin TB Joshua ya yi na baiwa wasu ‘yan jarida kudi domin bayyana cewar Jirgi ne ya bi ta kan Cocin kamin ta fadi.
Sai dai TB Joshua na shirin tafiya a Afruka ta kudu domin ganawa da hukumomin kasar kan wannan batu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.