Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana zargin Jonathan da soma yakin neman zabe kafin lokaci

Kungiyar Transformation Ambassadors of Nigeria da ke goyan bayan takarar shugaba Goodluck Jonathan ta kammala tarurukan ta a karshen mako a garin Benin wanda ya samu halartar jigajigan Jam’iyyar.  

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Masu sharhi kan siyasar kasar na bayyana tarurukan a matsayin riga malama Masallachi ganin ba’a kada gangar siyasa ba, yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin kaddamar da yakin neman zabe da bangaren shugaban kasar ya yi.

To sai dai mai bai wa shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa Farfesa Rufai Ahmed Alkali ya ce rashin fahimta ne ya kawo cece-kucen.

Yanzu haka dai akwai kungiyoyi da dama da ke ci gaba da yin kira ga shugaban da ya fito ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa zai tsaya takara a zaben na shekara mai zuwa, kuma tun irin wadannan kungiyoyi suka gudanar da tarurukan a shiyyoyi daban daban na kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.