Isa ga babban shafi
Nigeria

PDP ta damu dangane da ficewar Atiku Abubakar daga cikinta

Jam’iyyar PDP mai mulki a tarayyar Najeriya ta bayyana damuwarta a game da ficewar tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar daga cikinta zuwa jam’iyyar adawa ta APC.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya AFP / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A zantawarsa da Sashen Hausa na rediyo Faransa RFI, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP mai kula da shiyyar arewa maso yammacin kasar Ambasada Ibrahim Kazaure, ya bayyana cewa Atiku, mutum ne mai matukar muhimmanci ga PDP, domin kuma yana da magoya baya a sassa daban daban na kasar.

Kazaure, ya ce yanzu haka suna iya kokarinsu domin ganin cewa sun shawo kan tsohon mataimakin shugaban kasar domin dawowa a jam’iyyar ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.