Isa ga babban shafi
Najeriya

Wasu makarantun Najeriya sun fara aiki a wannan litinin

A Najeriya wannan litinin ita ce ranar da hukumomin ilimi na kasar suka bukaci a sake buda illahirin makarantun bokon kasar bayan kammala hutun karshen shekara.

Ministan ilimin Najeriya Ibrahim Shekarau
Ministan ilimin Najeriya Ibrahim Shekarau
Talla

To sai sakamakon bullar cutar Ebola a kasar hakan ya sa jama’a da dama na nuna shakku a game da komawa makarantar, kuma kamar yadda rahotanni ke nunawa wasu johohi sun ce ba za su buda makarantun a wannan litinin ba kamar dai yadda kungiyar malaman makaranta ta kasa ta bukaci a yi saboda a cewarta ba wasu matakai da gwamnati ta dauka domin kare malamai da dalibansu.

Jihar Lagos da ke kudancin kasar, inda cutar ta soma bayyana na daga cikin wadanda suka dauki matakin kin buda makarantar a yau.

Da farko dai ministan ilimi na kasar Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba za a buda makarantun ba sai a tsakiyar watan gobe na oktoba kafin daga bisani a rage kwanakin zuwa wannan litinin 22 ga watan satumba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.