Taron Afirka kan cutar Ebola a birnin Addis Ababa
Hukumar gudanarwa ta Kungiyar Tarayyar Afirka na gudanar da taro a wannan litinin domin samar da karin dubaru na yaki da cutar Ebola da ke ci gaba da kashe jama’a a yankin yammacin nahiyar.
Wallafawa ranar:
Taron wanda ke gudana a birnin Addis Ababa, na samun halartar wasu kwararri kan sha’anin kiwon lafiya daga kasashe daban daban na nahiyar, yayin da wasu tawagogi daga kasashen yammacin Afirka da ke fama da cutar za su yi wa taron karin bayani kan halin da ake ciki a yankin.
Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane fiye da 2000 sakamakon kamuwa da cutar a kasashen Liberia, Sierra Leone, Guinea Conakry da kuma Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu