AU ta kira taron gaggawa kan Ebola
Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta kira taron gaggawa a makon gobe don tattaunawa kan matsalar cutar Ebola da ta shafi kasashe biyar a Yammacin Afrika. Kungiyar tace taron da za’a yi a ranar litinin zai duba matsalar cutar da kuma dakatar da sufurin jiragen sama da jiragen ruwa da rufe iyakokin wasu kasashe da kyamar da ake nunawa mutanen da suka fito kasashen da ke fama da cutar Ebola.
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola sun haura 1,900 yanzu haka, inda ta gargadi kasashen da aka samu cutar da su dauki kwararan matakai.
Shugabar Hukumar Margareth Chan tace a cikin wanna makon an gano cewar adadin wadanda suka kamu da cutar a Guinea da Saliyo da Liberia sun kai 3,500, kuma 1,900 sun mutu.
Tace adadin ya tashi daga 1,552 da aka sanar sun mutu a makwannin da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu