Isa ga babban shafi
Ebola

Duniya ta gaza akan Ebola-MSF

Kungiyar bayar da agaji ta Likitocin da ake kira Medicins Sans Frontier, tace duniya ta gaza wajen magance cutar ebola da ke ci gaba da yi wa duniya illa, inda ta bukaci hadin kan masana kimiya don kai dauki ga kasashen Afrika ta Yamma. Wannan kuma na zuwa ne a yayin da wasu Fitattun shugabanin Afrika da Yan kasuwa da masana da suka hada da Olusegun Obasanjo suka rubuta wata budaddiyar wasika ga shugabanin Afrika akan daukar matakan dakile bazuwar cutar Ebola.

Isata Konneh wata mai dauke da cutar Ebola a kasar Saliyo
Isata Konneh wata mai dauke da cutar Ebola a kasar Saliyo UNICEF/Dunlop
Talla

A jawabin da ta yi wa Majalisar Dinkin Duniya, shugabar kungiyar Joanne Liu, tace watanni shida bayan barkewar annobar, duniya ta gaza wajen magance barazanar cutar

Shugabar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Margareth Chan ta bayyana cutar Ebola a matsayin barazana ga daukacin duniya.

Liu ta yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wajen samun kayayyakin aiki tare da tura kwarraru zuwa kasar Guinea da Saliyo da kuma Liberia inda cutar tafi kamari.

Wasu Fitattun shugabanin Afrika da Yan kasuwa da kuma masana da suka hada da Olusegun Obasanjo da Benjmain Mkapa da Graca Machel da Farfesa Ousmane Kane da Mamdou Diouf da dai wasu kusoshi 50 sun rubuta wata budadiyar wasika ga shugabanin Afrika akan daukar matakan dakile bazuwar cutar Ebola.

Wasikar da aka aikewa kafofin yada labaran duniya da dama cikin su har da Radio Faransa, na dauke da bukatar ganin shugabanin Afrika sun dauki matakai ganin yadda cutar ta ebola ke ci gaba da illa ga rayuwar Bil Adama da kuma tattalin arzikin Afrika ta Yamma.

fitattun mutanen sun bayyana matakan da aka dauka na rufe kan iyakoki da soke sauka da tashin jiragen sama a matsayin koma baya ga ci gaban kasashen Afrika.

Shugabanin sun bayyana goyan bayansu ga al’ummar Afrika kan wannan bala’I da ya shafi Yankin, inda suka bukaci aiwatar da matakan da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayayana, da kuma killace inda aka samu cutar,

Wasikar ta kuma bukaci shugabani da ‘Yan jaridu da masana da masu shirin fina finai da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan cutar.

A karshe shugabanin sun bukaci masana kiwon lafiya da masu bincike su taimaka wajen samo maganin cutar ta Ebola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.