Isa ga babban shafi
Ebola

Yawan jami'an lafiya dake kamuwa da Ebola na karuwa a Africa ta yamma

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace yawan jami’an kiyon lafiya masu kamuwa da cutar Ebola a yankin Africa ta yamma na dada karuwa bayan da a Najeriya aka samu karin wata mata da ta kamu da cutar sakamakon mutuwar mijinta, da shima cutar ce tayi sanadiyyar mutuwar shi.Wannan al’amarin dai na ci gaba da jan hankalin akasarin al’ummar yankin Nahiyar Afruka ta yamma inda aka ce hukumomi na kara daukar matakan dakile Cutar.Dama dai Hukumar lafiya ta Majalusar Dinkin Duniya ta yi kashedin cewar yawan masu kamuwa da ita wannan Cutar na dada karuwa musamman daga bangaren jami’an kiyon lafiya a kasashen Africa da cutar ta addaba.Hukumar ta ce fiye da ma’aikatan kiyon lafiya 120 ne suka mutu a yayin da wasu 240 kuma suka mutu sakamakon kamuwa da wasu cutuka masu alaka da Ebola.Zuwa yanzu Cutar ta Ebola ta hallaka mutane 1,552 daga cikin 3,062 da ta kama ya zuwa ran 26 ga watan Agustan da ya gabata.A kasar Guinea inda mutane 430 suka mutu, ma’aikatan kiyon lafiyar kasar sun shaidawa Kamfanin dillancin labarai na AFP cewar basu da kayan aiki.A kasar Senegal kuma yanzu haka likitoci na kulawa da wani matashi dan kasar Guinea da ya kasance na farko da aka sama da cutar a kasar, a yayin da mutane 694 suka mutu a Liberia.An ce akalla za’a iya kwashe Watanni 6 zuwa 9 kafin a samu nasarar magance cutar, da ka iya lakume Dalar Amurka miliyan 490, kuma kamin nan inji hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya akalla mutane 2000 na iya kamuwa.A jiya lahadi ma hukumomi a tarayyar Najeriya sun tabbatar da samun karin wata mata da ta kamu da Cutar a jihar River.Matar dai mijinta ya mutu a ran 22 ga watan Agusta bayan da shi ma ya kamu da ita. 

wani ma'aikacin lafiya dake yaki da cutar Ebola a kasar Liberia
wani ma'aikacin lafiya dake yaki da cutar Ebola a kasar Liberia REUTERS/2Tango
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.