Isa ga babban shafi
Ebola

Japan zata bayar da maganin cutar Ebola

Kasar Japan tace a shirye take ta gabatar da wani maganin gwajin cutar Ebola, da kanfanin kasar yayi domin anfani da shi wajen dakile cutar mai saurin yaduwa.Sakataren gwamnatin kasar Yoshihide Suga, yace a shirye kasar su take ta gabatar da maganin idan hukumar lafiya ta bukata.Ya zuwa yanzu dai babu wani maganin da ake iya tikaho da shi a matsayin rigakafi ko warkar da cutar ta Ebola.Sai dai an ga alamun samun nasara a wannan bangaren, bayan da wasu likitocin kasar Amurka 2 suka warke daga cutar, lokacin da aka basu maganin ZMapp da Kamfanin Mapp Bioparmaceutical na kasar ta Amurka daya sarrafa.Sai dai kuma yanzu Kamfanin na Mapp Bioparmaceutical yace maganin na ZMapp ya kare.Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO na ci gaba da tattaunawa, kan amfani da sabbin magungunan yaki da cutar ta Ebola, da zuwa yanzu ta lakume rayukan kusan mutane 1,500, tun lokacin da ta zama annoba a nahiyar Africa. 

Wasu masu bincike kan cutar Ebola
Wasu masu bincike kan cutar Ebola Reuters/Mariana Bazo
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.