Isa ga babban shafi
Lafiya

WHO tace sai a shekara mai zuwa maganin Ebola zai samu

Hukumar lafiya ta Duniya tace watakila cikin wata mai zuwa, a fara gwajin maganin cutar Ebola, da wani kamfanin kasar Britaniya ya sarrafa. Sashen bayar da rigakafi na hukumar lafiyan yace watakila sai shekara mai zuwa ta 2015 za a fara rarraba sabon maganin.Shugaban sashen bayar da rigakafi na hukumar lafiyan ta WHO Jean-Marie Okwo Bele yace za a fara gwajin sabon maganin cikin watan Satumba mai zuwa a kasar Amurka, kafin kuma a kai shi kashaen Africa, inda cutar ta Ebola ta tsananta.Dr Bele yace yana da yakinin sabon maganin zai wadata ga masu bukatar saye, kuma a sami sakakamako kan aikin shi, kafin karshen shekarar da muke ciki, kuma za a dauki matakan gaggawa wajen rarraba shi a shakarar 2015.Yanzu haka dai babu maganin cutar ta Ebola, dake sa zazzabi mai zafi, da zubar jinni a jikin bil Adama in ta tsananta, da kuma ta lakume rayukan a kalla mutrane 1,000 cikin wannan shekarar, a wasu kashen yammacin Africa.Masana sun ce cutar ta Ebola na iya sanadiyyar mutuwar kusan kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kamu, sai dai a baya bayan nan, kashi 55 zuwa 60 na wadanda suka kamu ne suka rasa ransu. 

wani ma'aikacin lafiya dake yaki da cutar Ebola a kasar Liberia
wani ma'aikacin lafiya dake yaki da cutar Ebola a kasar Liberia REUTERS/Samaritan's Purse
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.