Isa ga babban shafi
Lafiya

Kasashen yammacin Africa suna kokarin kawo karshen cutar Ebola

Annobar cutar Ebola da ta shafi kasashen Sierra Leone, Liberia da Guinée, na ci gaba da yaduwa a cikin kasashen, inda take barazanar haurawa ya zuwa wasu kasashen dake yammacin Afrika. Wannan yasa hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya neman kafa wata gidauniyar neman tallafin Dalar Amurka miliyan 100, domin yaki da cutar.Yau juma’a ne Shugabar Hukumar Lafiyar ta duniya, Dr Margaret Chan zata yi wata ganawa da wasu shugabanin kasashen yankin yammacin Afrika da cutar ta bulla, inda zasu kaddamar da wata guidauniyar neman tallafin, domin kare cutar daga ci gaba da yaduwa.Kawo yanzu cutar ta Ebola ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 730. A cikin wata sanarwa da hukumar ta lafiya ta fitar a a birnin Geneve shugabar hukumar Dr Margaret Chan ta ce, bisa la’akari da yadda annobar ke ci gaba da yaduwa a kasashen Laberiya Saliyo da Guinee, ana bukatar kara tashi tsaye wajen tunkararta, yin haka kuma a cewar ta, sai da kayan aiki da ke bukatar makudan kudade.Hukumar Lafiyan, tare da hadin gwiwar cibiyar yaki ta cututtuka ta kasar Amruka, CDC sun bayyana jerin wasu matakan kariya da taka tsantsan, wajen kare kai daga annobar ta Ebola. Ita dai annobar cutar ta Ebola, na haddasa zazzabi ciwon kai, da na jiki, ciwon gabobi da ciki, ga kuma mutuwar jiki, Amai da gudawa, rashin cin abinci da tsiyayar jinni.Sai dai kuma har yanzu masana kiyon lafiya na duniya na gudanar da bincike, don gano maganin cutar, amma kawo yanzu kokarin nasu ya ci tura.  

Likitocin MSF suna hada abincin da zasu baiwa masu cutar Ebola a kasar Saliyo
Likitocin MSF suna hada abincin da zasu baiwa masu cutar Ebola a kasar Saliyo Photo: Reuters/Tommy Trenchard
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.