Isa ga babban shafi
Ebola

Mutanen da suka mutu sakamakon Ebola sun doshi 1,500

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola a nahiyar Africa sun kai 1,427, cikin 2,600 da suka harbu. Wadannan alkaluman na nuna abinda aka kidaya daga watan Maris, lokacin da cutar tayi ta yaduwa, zuwa ranar 20 ga wannan watan na Oktoba, kuma a ranar talata da Laraba da suka gabata kawai, mutane 77 ne suka mutu sanadiyyar cutar.Cutar ta Ebola tafi yin illa a kasar Liberia, inda mutane 624 suka mutu, sai Guinea mai 406, yayinda 392 suka mutu a Saliyo.A Nigeria, inda wani dan kasar Liberia Patrick sawyer ya kai cutar, an rasa mutane 5.A halin da ake ciki kuma, cutar Ebola ta bulla a dukkanin yakunan kasar Liberia, yayin da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a iya shafe watanni kafin a iya shawo kan cutar.Hukumomin kasar ta Liberia sun ce mutane 2 sun mutu a lardin Sinoe, inda dama shine kadai bata isa ba.A farkon makon nan wasu matasa, dauke da kulake suka afkawa cibiyar da ake killace masu fama da cutar ta Ebola, inda suka yi awon gaba da katifu da kayan abinci, lamarin daya firgita majintan suka tsere.Sai dai daga baya dukkan marasa lafiyan sun koma cibiyar, don ci gaba da samun kulawa. 

Sashen da ake kebe masu fama da cutar Ebola a kasar Kenya
Sashen da ake kebe masu fama da cutar Ebola a kasar Kenya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.