Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola: WHO ta yi gargadi a Fatakwal

A wani rahoto da hukumar lafiya ta Duniya ta fitar tace akwai yiyuwar barkewar Cutar Ebola a birnin Fatakwal da ke yankin kudancin Nijeriya bayan mutuwar wani mutum da ya kamu da cutar A cewar hukumar akwai yiyuwar yaduwar cutar a wannan yankin da ke da dimbin arzikin man fetur, sakamakon mu’amalla da mutumin da ya mutu da cutar, ya yi da akalla mutane 255.

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO  Bruce Aylward yana magana game da yaki da cutar Ebola a Geneva
Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Bruce Aylward yana magana game da yaki da cutar Ebola a Geneva Reuters/路透社
Talla

Hukumomin Jihar sun ce sun tattara mutanen wuri guda a kokarin da suke yi wajen tantance lafiyarsu,

Wannan gargadin da hukumar ta lafiyar ta fitar game da yaduwar cutar ta Ebola a Najeriya ya sake jefa al’ummar kasar cikin wani sabon rudani, duk da ikirarin samun nasarar dakile cutar da ta bulla a jihar Lagos.

Rahotanni sun ce mutumin da ya shiga da cutar a Fatakwal ya yi mu’amalla da jama’a da dama, har ma ya gudanar da bikin haihuwar da ya samu a gidansa, abin da ke kara tabbatar da cewa ya yada cutar ta Ebola a garin.

Yanzu dai gwamnati Najeriya tare da Hukumar lafiya ta WHO hade da hukumar bunkasa ilimin da al’adu ta Majalisar Dinkin duniya UNESCO, da kungiyar ta Medecins Sans Frontiers, na cikin shirin ko ta kwana wajen nemo hanyoyin da zasu bayar da damar dakile cutar ta Ebola a birnin na Fatakwal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.