Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Kwamitin tsaro ya amince a tura dakaru a Afrika ta tsakiya

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin duniya ya amince da bukatar aikawa da dakarun wanzar da zaman lafiya 12,000 zuwa kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya inda ake ci gaba da rikici tsakanin Musulmi da Kirista.

Zauren Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya à New York
Zauren Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya à New York REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

Kasar Faransa ce ta gabatar da kudirin a gaban Kwamitin tsaro inda suka amince su tura da Sojoji 10,000 da ‘Yan sanda 1,800 zuwa Bangui da aka samu hasarar rayukan Jama’a da dama.

Amma sai a tsakiyar watan Satumba ne dakarun na Majalisar Dinkin duniya zasu isa kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya domin karbar ragamar tafiyar da aikin tsaro daga dakarun Faransa 2,000.

Akwai kuma dakarun Afrika sama da 6,000 da ake aikin wanzar da tsaro a Afrika tsakiya, amma dakarun Chadi sun ce zasu fice saboda yadda ake zargin suna nuna fifiko ga musulmi.

Dururuwan mutane ne aka kashe a rikicin Afrika tsakiya, Miliyoyan mutane ne kuma aka raba da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.