Chadi za ta janye dakarunta daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Taron shugabannin kasashen Afirka da na Tarayyar Turai da ke gudana a birnin Brussels, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kokarin da kasashen duniya ke yi domin dawo da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wallafawa ranar:
To sai dai kamar yadda aka ji a labaran duniya, yanzu haka kasar Chadi, wato daya daga cikin kasashen da ke taimakawa domin shawo kan wannan rikici ta ce za ta janye dakarunta daga kasar.
Kasar Chadi dai ta bayyana daukar wannan mataki ne domin nuna bacin ranta dangane da abin da ta kira shi da suna cin zarafi da kuma bita da kulli da ake yi wa kasar, duk kuwa da kokarin da take na samar da zaman lafiya a can karkashin inuwar MDD.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu