Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Harin gurneti ya kashe Mutane 20 a Bangui

Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, bayan da wasu mahara suka wurga gurneti a wajen wani taron zaman makoki. Ministan tsaron kasar, Denis Wangao Kizimale, yace harin ya raunata wasu mutane goma sha daya, wadanda a yanzu haka suke karbar magani a asibiti.

Dakarun Sojin Faransa da na Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Dakarun Sojin Faransa da na Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika REUTERS/Luc Gnago
Talla

Tun a watan Maris din bara, kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya rikici ya barke a kasar mai nasaba da addini tsakanin Musulmi da Kirista.

Gwamnatin kasar tace ‘Yan ta’adda ne suka kai harin, amma babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin.

Rikicin kasar dai ya kazance, a lokacin da mayakan anti-balaka kiristoci suka fara kai hare haren fansa kan musulmi bayan mayakan Seleka musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.