Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Afrika ta tsakiya: AU ta saka ‘Yan anti-bakala cikin ‘Yan ta’adda

Kungiyar Tarayyar Afrika ta saka Mayakan sa-kai na anti-balaka cikin Kungiyoyin ‘Yan ta’adda wadanda ke kai wa Musulmi hari a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, wannan kuma na zuwa ne bayan sun kashe wani Sojan wanzar da zaman lafiya na Jamhuriyar Congo.

Makamai da aka karbe daga hannun Mayakan anti-balaka a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Makamai da aka karbe daga hannun Mayakan anti-balaka a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya REUTERS/Sia Kambou/Pool
Talla

Kungiyar ta bayyana damuwa akan rikicin Afrika ta tsakiya duk da Sojojin Faransa kusan 2,000 da na Afrika 6,000 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

A ranar Litinin ne mayakan anti-balaka suka kashe wani Sojan kasar Congo a Boali da ke kusa da Bangui. Akwai kuma mayakan na Anti-Balaka da dakarun Afrika suka kashe guda 12.

A cikin sanarwar, kungiyar Tarayyar Afrika tace zata dauki mataki musamman Sojoji MISCA 21 da aka kashe wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya.

Tun lokacin da Mayakan Seleka mafi yawancinsu Musulmi suka hambarar da gwamnatin Bozize a Bangui, Mayakan anti-balaka, Kiristoci suka rungumi makamai domin mayar da martani.

Zuwa yanzu dubban mutane suka mutu, daruruwa ne kuma suka gujewa gidajensu sakamakon kazancewar rikicin Afrika ta tsakiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasata cewa kimanin musulmi 15,000 suka makale a Bangui da wasu yankunan arewacin kasar, wadanda ke karkashin kulawar Sojojin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.