Shekara daya cur da kifar da gwamnatin Francois Bozize
A kawana a tashi yau 24 ga watan Maris shekara daya kenan da kifar da shugaba Francois Bozize daga karagar mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wallafawa ranar:
Kawancen ‘yan tawayen Seleka ne dai ya kori Bozize daga karagar mulki, bayan share tsawon watanni ana fama da yakin basasa a kasar, inda suka daga bisani aka dora Michel Djotodia a matsayin shugaban kasa na riko.
To sai dai sakamakon tashe-tashen hankulan da aka ci gaba da samu a kasar, wannan ya sa shugabannin kasashen yankin Tsakiyar Afrika sun gudanar da taro a birnin Ndjamena na kasar Chadi tare da tilasta masa sauka daga kan mukaminsa.
Saukarsa daga kan wannan mukami ke da wuya sai sabon rikicin ya barke, inda aka samu bayyanar kungiyar ‘yan Anti-balaka wadda ta kunshi kistoci tsintsa, kungiyar da kai hari kan musulmi wadanda take zargi da marawa Djotadia baya. Kasar Faransa da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun gargadi kungiyar ta Anti-balaka da ta kawo karshen yadda take kashe musulmi a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu