Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Mutane 30 sun mutu a rikicin Afrika ta tsakiya

Rahotanni daga kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya sun ce akalla fararen hula 30 suka gamu da ajalinsu, a wani rikici da ya kaure tsakanin kiristoci da musulmi. Rundunar ‘yan sandan kasar na cewa wasu mutane 10 suka sami raunuka sakamakon rikicin da ya barke a garin Dekoa .

Dakarun Afrika da ke aikin  Wanzar da zaman lafiya na MISCA a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Dakarun Afrika da ke aikin Wanzar da zaman lafiya na MISCA a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya REUTERS/Siegfried Modola
Talla

‘Yan sanda sun ce Mayakan anti-balaka ne Kiristoci suka kai wa ‘Yan kungiyar Seleka Musulmi hari.

Kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne bayan da mayakan Seleka suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize wanda ya kwashe shekaru sama da 10 yana mulki.

Mayakan anti-balaka sun kaddamar da hare haren fansa ne kan Mayakan Seleka, lamarin da har ya sa Djotodia ya yi murabus.

An kashe dubban mutane a rikicin kasar, kuma dubun dubatar mutane ne suka fice daga kasar zuwa makwabtan kasashe.

Akwai Dakarun Faransa da na Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya kuma Jami’an tsaron samar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Turai (Eufo) sun fara isa Bangui domin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.