Isa ga babban shafi
Mali-Burkina Faso

Mayakan Ansar Dine sun bude kofar tattaunawa don magance rikicin Mali

Shugaban kungiyar Ansar Dine Iyad Ag Ghaly, wanda ke bukatar tabbatar da Shari’ar Musulunci a kasar Mali, yace zai goyi bayan matakin sasantawa domin kawo karshen rikicin siyasar kasar Mali bayan ya gana da Ministan Harakokin wajen Burkina Faso Djibrill Bassole a birnin Kidal da Gao.

Ministan harakokin wajen Burkina Faso  Djibril Bassolé, tare da Shugaban kungiyar Ansar Dine, à  birnin Kidal.
Ministan harakokin wajen Burkina Faso Djibril Bassolé, tare da Shugaban kungiyar Ansar Dine, à birnin Kidal. AFP PHOTO / RPMARIC HIEN
Talla

A jiya talata ne, Ministan harakokin wajen kasar Burkina Faso Jibril Basole ya kai ziyara kasar Arewacin Mali da ke karkashin ikon Mayakan Ansar Dine a wani mataki da kasar Burkina Faso ke yi na kokarin shiga tsakanin rikicin Mali.

Bayan ganawa da shugabanin Ansar Dine, Mista Bassole yace akwai alamun warware matsalar kasar ta hanyar tattaunawa, maimakon amfani da karfin soji.

A lokacin tattaunawa da ministan Burkina Faso a Kidal Shugaban kungiyar Ansar Dine Iyad Ag Ghaly, ya bada goyon bayansa ga shiga tsakanin da shugaban kasar Burkina Faso ke yi, karkashin kungiyar kasashen yammacin Afrika ta CEDEAO ko ECOWAS.

A gaban tarin ‘Yan jaridu, a cikin babbar riga mai kalar hazo da farin rawaninsa shugaban Ansar Dine, yace sun gamsu, tare da yarda da shiga tsakanin Shugaba Compaore.

Sai dai kuma Iyad Ag Ghaly bai bayyana matsayin da kungiyarsa ta Ansar Dine da ke bukatar kafa shari’ar musulunci a daukacin fadin kasar Mali zata dauka a lokacin tattaunawar ba, kamar yadda a nata bangaren kungiyar MUJAO da ke kawance da Al ka’ida reshen Maghreb ta ki ta yi furuci dangane da matsayinta a tattaunawar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.