Isa ga babban shafi
Mali

An yi Arangama tsakanin matasa da mayakan Ansar dine na Mali

An yi wata Arangama tsakanin Matasa da mayakan kungiyar Ansar Dine a garin Gao da ke arewacin Mali bayan matasan sun fito domin adawa da hukuncin yankewa wani hannu da ake zargin dan fashi da makami ne.

Mayakan kungiyar Ansar Dine a Arewacin Mali
Mayakan kungiyar Ansar Dine a Arewacin Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

Rahotanni sun ce, daruruwan mutane ne suka shiga zanga zangar adawa da hukuncin, al’amarin da ya sa ‘Yan kungiyar suka harba harsashe a sama, wanda kuma ya raunana wasu mutane, cikinsu har da wani Dan Jarida, Malick Aliou Maiga.

Rikicin ya biyo bayan hukuncin jifa da aka yanke wa wasu da aka kama da laifin Zina karkashin Shari’ar Musulunci da kungiyar Ansar Dine ta girka a Garin na Gao.

Jami’an kiwon lafiya a Asibiti sun ce mutane Shida ne suka samu rauni.

Garin Gao yana cikin biranen da suka fado karkashin ikon kungiyar Ansar Dine da ke fafutikar tabbatar da Shari’ar musulunci a kasar Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.