Isa ga babban shafi
Mali

Hafsoshin Kasashen Sahel na Afrika suna taro akan Mali

Hafsoshin Sojan kasashen Sahel na Africa na taro a Mauritania domin nazarin tabarbarewar tsaro a yankin kasar mali.Mahalarta taron sun fito daga Mauritania, Algeria, Mali da Niger, na taron nasu ne cikin sirri.  

Wasu shugabannin kasashen Sahel a Afrika
Wasu shugabannin kasashen Sahel a Afrika AFP/Stringer
Talla

Bayanai na cewa zasu taimakawa kasar Mali maido da mutunci da darajar ta.

Hafsoshin sun kuma tattauna yadda za a kafa wata rundunar sojoji daga kasashen guda hudu.

Kasar Mali a da na daga cikin kasashe masu daurarriyar demokradiya, amma juyin mulki da sojoji su ka yi, kasar ta shiga rudani.

Masu fafutukar Islama a kasar sun kafa shari’ar musulunci inda su ka rurrusa wasu wuraren tarihi wanda su ka ce sun sabawa addinin Islam.
 

Hakan kuma ya jawo alwadai daga kasashen duniya.

Gwamnatin rukon kwarya da aka kafa bata yi tasiri ba saboda kungiyoyi da ke dauke da makamai da ke dawo da hanun agogo baya.

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika sun bada umurni kasar ta Mali ta yi kokari ta kafa gwamnati wacce za ta tafi da kowa da kowa daga nan zuwa 31 ga watan Yuli.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.