Isa ga babban shafi
Alka'ida-Sahel

kasashen duniya na biyan diyya ga kungiyar Alka'ida ta yankin sahel

Wani rahoto kan tsaro a yankin sahel ya bayyana cewa, kasashen da kungiyar Alka’ida a yankin Sahel (Aqmi) ta yi garkuwa da ya’yansu, na biyanta diyya kafin ta saki yayan nasu, inda rahoton ya nemi kasashen da su hada kansu, domin kaucewa hadarin da ke tattare da haka.Rahoton ya bayyana cewa, kasashen basu fadar cewa sun biya kungiyar ta Alka’ida diyya, amma sanin kowa ne suna biyan kudade, har ma da ita kasar Amruka, idan ma ba a biya kudin a gwamnatance ba, to za’a tarar wasu kamfanoni ne masu zaman kansu ke biyan diyyar, kamar yadda dan majalisar dokokin kasar Fransa Francois Loncle ya sanar da manema labarai a yau, gutsier daga cikin rahoton dangane da shi’anin tsaro a yankin Sahel, rahoton da za a fitar nan gaba.A cikin rahoton an bayyana cewa, kashi 90% na kudaden shigar da kungiyar ta alka’ida yankin Sahel Aqmi ke samu, ya na fitowa ne daga diyyar da ake bata, domin sakin wadanda ta yi garkuwa dasu.An kuma bayyana cewa, a baya kungiyar ta bukaci bata Euros miliyan 90 domin sakin faransawa 4 da ta yi garkuwa dasu a cikin watan September 2010 da ga kasar jamhuriyar Niger. Kudin da suka zarta tallafin shekara da Faransa ke baiwa kasashen Niger da Mali. 

Imagens mostradas pelo canal de TV al-Andalus no dia 30 de setembro de 2010, onde aparecem os sequestrado francês Françoise Larribe, à direita.
Imagens mostradas pelo canal de TV al-Andalus no dia 30 de setembro de 2010, onde aparecem os sequestrado francês Françoise Larribe, à direita. AFP/Al-Andalus
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.