Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An gano Budurwa da aka sace tun tana jaririya

Bayan shafe shekaru 17, a kasar Afrika ta kudu an gano wata yarinya da aka sace tun tana jaririya a hannun mahaifiyarta a lokacin da ta ke bacci bayan an haife ta a wani Asibiti, kamar yadda ‘yan sandan kasar suka tabbatar.

Reuters
Talla

A bana ne Yarinyar ta hadu da ‘yar uwarta da suke kama a makaranta guda, daga nan aka fara gudanar da bincike har aka gano ‘Yan uwan juna ne.

Yarinyar mai suna Zephany, duk shekara iyayenta suna gudanar da bikin haifuwarta, tun lokacin da aka sace ta.

Rahotanni sun ce Zepahny ta girma tare da wasu iyayen amma ba tare da sanin ‘yarsu ba ce.

Zephany ta hadu da iyayenta na asali ne bayan ta raka Cassidy gida saboda shakuwar da suka yi domin an ce suna kama da juna.

Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun cafke matar da ta sace ta mai shekaru 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.