Isa ga babban shafi
New Zealand

Wata mace ta yi ta shayar da jaririn ta wiwi

Wata mace ‘yar kasar New Zealand ta amince da cewa ta baiwa jaririn ta mai watanni 3 da haihuwa tabar wiwi ta nonon ta. Rahotannin da ke fitowa daga kasar yau Asabar na cewa an yanke wa matar mai shekaru 29, da ke zaune a garin Wanganui, hukuncin daurin jeki ki gyara halin ki, na watanni 6.‘yan sandan da suka gurfanar da ita sun ce sun je canjin gidan ne suka gano abin da matar ke aikata wa, inda ta amsa laifin nata, don haka suka caje ta, da cin zarafi yara. 

Hoton wani jariri
Hoton wani jariri Reuters/Ukrainian Border Service/Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.