Isa ga babban shafi
KYRGYZSTAN

Mutane kusan 100 sun hallaka cikin rikicin kabilanci

Tashin hankalin daya ritsa da yankin kudancin kasar Kyrgyzstan, ya hallaka kusan mutane 100, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.Shaidun gani da ido sun ce dakarun kasar sun bude wuta akan masu kawo tashe tashen hankulan na kabilanci.Dubban mutane sun tsere daga garin Osh, inda gwamnati ta baiwa dakaru umurnin amfani karfi. Tuni gwamnatin kasar Russia tace bata da shiri shiga kasar domin kwantar da wutar rikicin, kamar yadda gwamnatin riko ta kasar ta Kyrgyzstan ta bukata.Fiye da mutane dubu 32 ke gudun hijira sakamakon wannan rikici da ya barke. Babban Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwa da halin da mutane suka samu kan su a ciki, sanadiyar rikicin mai nasaba da kabilanci. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.