Isa ga babban shafi
Kyrgyzstan

Mutane 23 sun hallaka sakamakon rikici mai nasaba da kabilanci

Mutane 23 suka hallaka sakamakon rikicin kabilanci da ya rita da yankin kudancin kasar Kyrgyzstan, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar.Rikicin ya kaure a garin Osh, inda ya zama lamari mafi muni da kasar ta yankin Tsakiyar Asia ta fuskanta tun bayan girka gwamnatin riko cikin watan Afrilu.Gwamnatin rikon karkashi jagorancin Roza Otunbayeva, ta kafa dokar ta baci cikin yankuna hudu na kasar, sanadiyar rikic tsakanin matasa dake dauke da makamai, tare da tura dakaru, masu aikin tabbatar da zaman lafiya.Wannan sabon rikicin ya balle cikin yankin kudanci inda hambararren shugaban kasar Kurmanbek Bakiyev, ke da karfi.Tuni aka far kirar neman samun zaman lafiya, kuma jakadan Amurka dake kasar ta Kyrgysztan, yana cikin masu kirar samun zaman lafiyar.Mutane 23 sun hallaka, yayin da wasu kusan 300 suka jikata, sakamakon rikicin na yau Jumma’a.

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.