Isa ga babban shafi
Burundi

Rikici na ci gaba da zafafa a Burundi

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya dage ranar zaben ‘Yan Majalisu zuwa watan gobe, lamarin da ya haifar barkewar sabuwar zanga-zanga a kasar. Rikicin kasar Burundi dai na ci gaba da zafafa, yayin da rahotanni ke cewa ‘yan sandan kasar sun harba harsashe da hayaki mai sa kwalla domin tarwasa masu zanga-zangar adawa da matakin shugaba Nkurunziaza na neman wa’adi na uku.Rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka fito kan tituna suna zanga-zangar, bayan gwamnatin Shugaba Nkurunziza ta sanar da dage zaben ‘Yan majalisu zuwa 5 ga watan Yuni, maimakon ranar 26 ga watan nan na mayu.Masu zanga-zangar dai yanzu na neman Nkurunziza ya yi murabus, ko ya ja gefe ba tare da neman wani wa’adin mulki ba.Rahotanni kuma na cewa rikicin Burundi ya koma tsakanin Sojojin da ke biyayya ga gwamnati da kuma bangaren wadanda suka jagoranci juyin mulki a makon jiya.A yau Laraba wani dan sanda ya harbe wani soja har lahira, lamarin da ke kara haifar tsoro da fargaba tsakanin al’umar kasar na rikidewar rikicin siyasar kasar zuwa yakin basasa. 

Masu zanga Zanga sun cinna wuta kan titi a kasar Burundi
Masu zanga Zanga sun cinna wuta kan titi a kasar Burundi REUTERS/Goran Tomasevic
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.