Burundi na barazanar murkushe masu zanga-zanga
Gwamnatin Kasar Burundi ta yi barazanar amfani da sojoji don murkushe masu zanga zangar adawa da shirin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na neman wa’adi na uku sabanin yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Ministan tsaron kasar Janar Pontien Gaciyubenge, ya ce aikin sojojin ne su tabbatar da tsaro kuma duk lokacin da shugaban kasa ya ba su umurni za su aiwatar.
Wallafawa ranar:
A ranar juma’ar da ta gabata an yi taho mu gama tsakanin ‘Yan Sanda da masu zanga zangar da suka fito daga Jam’iyyu 6 na kasar inda aka kama mutane 65 daga cikinsu tare da tuhumarsu da laifin yin tawaye.
A watan Juni al’ummar kasar Burundi za su jefa kuri’ar zaben shugaban kasa inda ‘yan adawa da kungiyoyin fararen hula ke kokarin haramtawa shugaban kasar mai ci yin tazarce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu