An yi arangama tsakanin ‘Yan sandan Burundi da mabiya darikar Katolika
Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu a wata arangama da ‘Yan sandan kasar Burundi suka yi da wata kungiyar mabiya Darikar Katolika da ke karrama wata mata da ake kira Zebiya.
Wallafawa ranar:
Rikicin ya barke ne da sanyin safiya inda daruruwan mabiya kungiyar wata mata da ake kira Zebiya wadanda ‘Yan asalin darikar katolika suka yi arangama da ‘Yan sandan kasar Burundi, a yayin da suke kokarin isa kan wani tsauni da suka mayar wajen kai ziyara domin girmama matar.
Akalla mutane shida ne suka mutu a cewar Gwamnan yankin Kayanza, inda anan ne lamarin ya faru, wasu mutane 35 daban suka samu raunuka.
Kodayake ‘Yan sanda hudu sun samu munanan raunuka, a arangamar, sai dai Gwamnan yankin na Kayanza, Athanase Mbonabuca ya ce dukkanin wadanda suka mutu daga bangaren mabiya kungiyar ta Zebiya ne a yayin da a yanzu haka wasu daruruwa ke hannu.
Rahotanni na nuna cewa dangantaka tsakanin ‘Yan kungiyar ta Zebiya da Mujam’iar Katolika a ‘yan watanni nan na kara tabarbarewa.
A watan Disambar bara ne ‘Yan sanda suka tarwatsa wani gini da ‘Yan kungiyar suka yi a kan tsauni da suka mayar da shi wajen ibada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu