Burkina Faso
Burkina ta fara binciken sanadin mutuwar Sankara
Kasar Burkina faso ta kaddamar da bincike domin gano dalilin kisan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara a shekarar 1987 kamar yadda iyalansa suka bukata. Lauyan iyalan tsohon shugaban Benewende Sankara ya ce wani alkalin soja ne ke gudanar da binciken yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Talla
A farkon wannan watan na Maris ne gwamnatin Burkina Faso ta bayar da umurnin tono gawar shugaban domin gudanar da bincike.
Hambararren shugaban kasar ne Blaise Campaore ake zargi da kashe Sankara, yayin juyin mulkin da ya kawo shi karagar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu