Kotun Burkina ta ki bayar da umurnin a tono gawar Sankara
Babbar Kotun kasar Burkin Faso ta yanke hukuncin cewa ba ta da hurumin yanke wata kara da aka shigar gabanta da ke neman a sake tono gawar tsohon Shugaban kasar na soja Thomas Sankara.
Wallafawa ranar:
Matakin kotun ya harzuka dangi da ‘yan uwan tsohon Shugaban wanda aka kashe a juyin mulkin da aka gudanar a 1987 da ya kai ga shugaba mai ci yanzu Blaise Campore hawa kujeran Mulki.
A wancan lokaci marigayi Thomas Sankara da wasu manyan sojoji 14 aka kashe tare da yin gaggawar binne su ba tare ‘yan uwa da dangin sun yi tozali da gawawwakinsu.
A shekara ta 2010 ne dangi da ‘yan uwan mamatan suka nemi kotu ta bayar da izini a tono gawarsu domin a gudanar da bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu