Isa ga babban shafi
Tennis

Roland-Garros: Federer ya sha kashi hannun Tsonga, Willams ta je zagaye na gaba

A gasar kwallon Tennis ta French Open ko kuma Roland-Garros da ke gudana yanzu haka a birnin Paris na kasar Faransa, a karawar da aka yi jiya talata, Jo-Wilfried Tsonga dan kasar Faransa, ya doke Roger Federer dan kasar Suisse, wanda hakan ya bai wa Bafaranshen damar zuwa zagayen da ke biye wa na karshe a bangaren maza.

dan wasan Tennis na Faransa, Jo-Wilfried Tsonga.
dan wasan Tennis na Faransa, Jo-Wilfried Tsonga. Reuters
Talla

Jo-Wilfried dai ya doke Federer ne ci 7-5, 6-3, 6-3.
A ranar juma’a mai zuwa ne dai wannan Bafarashe zai kara da David Ferer dan kasar Spain wanda a yau ke rike da matsayin na hudu a sahun ‘yan wasar Tennis na duniya, idan kuma ya yi nasara a wannan haduwa, ana kyautata zaton cewa Jo-wilfried zai kara a zagayen karshe ne tsakaninsa da Rafael Nadal ko kuma Novak Djokovic.
 

To a bangaren mata kuwa, Serena Williams ‘yar kasar Amurka ta samu nasarar zuwa zagayen da ke biye na karshe a wannan gasa, bayan da ta samu nasara a kan abokiyar karawarta a Svet-lana Kuznetsova ‘yar kasar Rasha a jiya, sun kuwa tashin wasar ne ci 6-1, 3-6, 6-3.

Wannan nasara dai, ta bai wa Williams kwarin gwiwa a kokarin da take na sake daukar kofin gasar ta Roland Garros karo na biyu a tarihi, domin kuwa ta taba daukar kofin a shekara ta 2002.

Serana Williams dai za ta kara ne da Sara Errani ‘yar kasar Italiya a gobe alhamis, wadda ta samu zuwa wannan matsayi bayan da ta doke ‘yar kasar Polond mai suna Agnieszka Radwanska.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.